Followers

Tuesday, March 28, 2023

Rayuwa Ba Tabbas

      ☆via-the2brothers-links☆

MENENE NAKA NA KA YI TA RIGIMA DA RAYUWAR DA KAIMA BAKA DA TABBAS DA ITA?



-Sheikh Ibrahim Zakzaky (H)


"In mutum ya duba da kyau sai ya ga duniyar nan bata cancanta ma a ce mata rayuwa ba, rayuwa wacce take bata da tabbas cewa zaka kai wani lokaci nan gaba, baka da garanti din cewa badi kana nan, ko kana da shi? baka da garanti din zaka kai watan gobe, ko makon gobe, kai ko gobe ma, kai baka da garanti ma koda na shakan numfashi ko kiftawan ido, domin tsakanin kiftawan ido ana iya zare maka rai.


"Nasan wani mutum a unguwar mu da ya yi wani mutuwa da ya firgita wasu mutane. Ana zaune a gindin wata itaciya sai yace yau gobe kwana na uku banyi kaa..., kafin yace Shi, ya mutu. Da yace ka dinnan kawai sai ya tafi, sai aka ga gawa kawai ya kife, mutanen da suke zaune abin ya basu mamaki To Allah ta'ala yana iya daukan ranka tsakanin wannan, tsakanin kalma daya mai harufa biyu baka da garanti ko na kiftawan ido, to menene naka na kayi ta rigima da rayuwan da kaima baka da tabbas da ita. 



@SZakzaky'sGallery

No comments:

Post a Comment