Followers

Tuesday, March 28, 2023

Rayuwa Ba Tabbas

      ☆via-the2brothers-links☆

MENENE NAKA NA KA YI TA RIGIMA DA RAYUWAR DA KAIMA BAKA DA TABBAS DA ITA?



-Sheikh Ibrahim Zakzaky (H)


"In mutum ya duba da kyau sai ya ga duniyar nan bata cancanta ma a ce mata rayuwa ba, rayuwa wacce take bata da tabbas cewa zaka kai wani lokaci nan gaba, baka da garanti din cewa badi kana nan, ko kana da shi? baka da garanti din zaka kai watan gobe, ko makon gobe, kai ko gobe ma, kai baka da garanti ma koda na shakan numfashi ko kiftawan ido, domin tsakanin kiftawan ido ana iya zare maka rai.


"Nasan wani mutum a unguwar mu da ya yi wani mutuwa da ya firgita wasu mutane. Ana zaune a gindin wata itaciya sai yace yau gobe kwana na uku banyi kaa..., kafin yace Shi, ya mutu. Da yace ka dinnan kawai sai ya tafi, sai aka ga gawa kawai ya kife, mutanen da suke zaune abin ya basu mamaki To Allah ta'ala yana iya daukan ranka tsakanin wannan, tsakanin kalma daya mai harufa biyu baka da garanti ko na kiftawan ido, to menene naka na kayi ta rigima da rayuwan da kaima baka da tabbas da ita. 



@SZakzaky'sGallery

Monday, December 12, 2022

12 December

 THE BLACK DAYS



12th to 14th December, 2015 could be seen as Black Days in the history of the giant of Africa, Nigeria. The days witnessed a stream of blood ocean flowing through various streets of the Zaria City in Kaduna State of Northern Nigeria, as the Nigerian Army appeared there, armed to the teeth and crushed on armless and peaceful citizens (that are exercising their constitutional freedom of religion and the right of peaceful assembly enshrined in the Constitution of the Federal Republic of Nigeria, 1999 as amended).


The Army that are equipped and paid from the Public Treasury to defend /protect Nigerians ended up in extinguishing more than a thousand innocent citizens. They inhumanely massacred 193 children (including a one and half year baby), 97 women (of which 23 were pregnants), 548 men and about 39 families completely wiped out of existence. They took and gave all the corpses mass burial denying their families the right to observe proper funeral /burial rites. 


As a result of the massacre, 170 undergraduate students were murdered, 2,189 children became orphans, 519 women became widows and about 1,104 parents lost their children.


The Army committed heinous crimes that included setting fire to buildings, burning people alive amd shooting infants at close range among others.


All these were orchestrated under the command of some scoundrel elements in authority who appeared to have given preference to their selfish interest /sectarian bigotries over and above the Laws of the Land.

         Sheikh Zakzaky's house 


Lastly, The perpetrators of this crime have to be brought in to book as recommended by kangaroo JCI established by Kaduna State Government.


#We_Say_No_To_Oppression!

#No_To_Injustice!

#No_To_Crime_Against_Humanity!

#Justice_For_Zaria_Victims!


via-the2brothers-links 

Tuesday, March 5, 2019

"A yayin da Shaikh Zakzaky ke kokarin saka rawani, suna rirrike shi suna kokarin fita da shi da karfi. Da kyar Shaikh ya samu ya saka takalminsa a yayin da suke jan sa, ba su bari ya saka abayarsa ba sai bayan da suka fito da shi."

"Haka suka fito da Shaikh Zakzaky suna rirrike da shi, ba su dubi tsufansa a matsayinsa na Dattijo mai shekara 67 ba, ba su yi la’akari da raunukan da ke jikinsa na harbin da sojoji suka masa a kafa, hannu da ido ba, suka rika musguna masa, har suka san ya shi a tsakiyar mota a baya, gefe da gefensa a cikin motar akwai jami’an tsaro kowanne rike da bindiga har da bindigar da suke saka wa mutum ta yi masa shokin".

- Mun kwafo daga Jaridar Almizan bugu na 1382 ne.




Batun waqi,ar zariya

SHAIKH ABDULJABBAR YACE:

 JIYACE TA DAWO YAU>>>>

Tarihi Ne Yake Maimaita Kansa hakanan akayiwa Fatima "yar Annabi (s) da Imam Ali Zakin Allah Kani Kuma Sirikin
Annabi(s) Kuma Aka bi 'ya'aynsu Da Jikokinsu Da Mabiyansu Akayi Musu Kisan Gilla Wasu Aka Basu Guba Wasu Aka Qonasu Da Ransu Wasu Aka Binnesu Da Ransu Kuma Akama Halasta Zaginsu Da
Tsine Musu>>>
Kuma Akace Baza Afa'da ba Duk
Wanda Ya Fa'da Ya Zagi Sahabbai, Kuma Duk Wanda Sukayi Wannan Aika-aikar Akace Sunyi Daidai Kuma Su Radhiyallahu Anhu Ne...
QARSHE SAI ALLAH NE YAYI HUKUNCINSA>>> 

To yanzuma jiya ce ta dowa yau kwabo-kwabo abinda akayi
wancan lokacin shine ake ciki yanzu... Wanda sukayiwa 'yan shi,a wannan ta,asar ance sunyi daidai kuma baza ace damme yasa ba an zagi shugabannni kuma su Allah Ya Yarda Dasu >>>
Kuma Wanda Aka Zalunta Wai Bazasuyi Qorafi ba Kuma Bazasuyi Wata Walwala ba.

TO DA ALAMA WANNANMA ALLAH NE ZAIYI HUKUNCINSA....

01/Rabi'ul Auwal/1437.

KAMAR MAKKAH KAMAR ZARIYA A RAN ƊAYA GA RABI'IL AUWAL 1437


Mahangar Shi'a ba tare da alfahari ba tana ƙunshe da nazarin da wata mahanga ba ta da shi, sannaj kuma ta keɓanta da al'amura da suke da dalili a hankalce saɓanin mafi yawan ra'ayoyin sauran mazhabobi da addinai.


YIWUWAR MAIMAICI:

Idan ma'aunin ilimi shi ne karɓar maimaici, to irin tashin Imam Mahdi (A) da tsayuwarsa don kafa daular adalci ta faru a lokuta masu yawa a zamanin farko kamar sauran sunnonin Allah. Don haka hukumarsa zata kasance wani ɓangare ne na sauran da suka gabata, tafarkin Imam Mahdi (A) da zuwan sa yayi kama da irin zuwan Annabi Musa (A), da Isa (A) da Muhammad (S)


Idan haka ne: Shin zai zama abin mamaki idan Allah ya kawo wani Musan wannan zamanin watau Imam Mahdi (A) da zai kawar da zaluncin da adalcinsa? da kuma taimaka masa da Harunansa zai yi, wato Annabi Isa (A), domin su kwance raunanan mutane daga ƙangin ɗaurin Fir'aunan zamani, su tseratar da su daga Dujal mai sihiri? Shin zai zama abin mamaki domin Allah ya sake tayar da wani mai tseratarwa ga ɗan Adam kamar yadda Muhammad Musɗafa (S) ya zo yana mai cewa: Kuce La'ilaha illallah!

( Shi'anci Da Duniyar Gobe. shafi na 106. littafin Dakta Ayat Kambari,  Fassarar Dakta Hafiz Muhammad Sa'id Kano)


In mukayi la'akari da abin da ya gabata daga littafin Shi'anci da Duniyar gobe, na yiwuwar samun maimaicin lamura a  rayuwar ɗan adam, za muga cewa a wannan yankin na  ƙasar tamu  an taɓa samun wani Mujaddidi da ya sabunta lamarin addini a wannan nahiyar aka wanzu a  cikin adalcin mahalicci. Haƙiƙa ba abin mamaki bane sake ganin wani da zai maimaita wancan yanayin na Shehu Usman ɗan Fodiye da ya gabata sama da shekatu 200.


Maganar Sayyid Zakzaky, in muka lura , domin bayan ya fara kira akan kalmar Tauhidi, (Babu hukuma sai ta Allah)  wannan ya karɓu har tafiyar ta koma Jafariyanci to ya ci gaba da kira ne akan tabbatar da adalci, da rushe zalunci ga kowane ɗan Adam ba lallai Musulmi ba. Wanda shi ya janyo a yanzu haka cikin tafiyar ta haɗa da Shi'a da Sunna, da ma wasu addinin Kitistanci harma da waɗanda suke musanta samuwar Allah daga masu ƙyamar zalunci sunantarr da harkar da Saiyid Zakzaky ke jagoranta a Nijeriya. Don gwagwarmayar kuɓutar da al'umma daga zaluncin da suke ciki. Wanda wannan shine farko tushen da Imamul-Hujjah (A) zai yi yaƙi a kai, na kawar da azzalumai da zalunci da tallafawa waɗanda ake zalunta na duniya baki ɗaya daga kowane tafarki. Shi yasa ma hadisai suka tabbatar har da Kiristoci a mataimakansa da masu bautar rana, don haka ne a na kusa da shi Imam Mahdi (A) Masihu Isa ɗan Maryam(A) ne  ga kuma Khidir (A).


Haƙiƙa tarihi yakan maimaita kansa ta fuskoki da daman gaske. Domin ita wannan rayuwar takan jujjuya ne a tsakain mutane. Watau akan samu maimaicin yanayin rayuwa a tsakanin wata al'ummar da wata data biyo bayanta a wani zamanin ko ƙarni a wani lokaci ta wasu fuskokin walau iri ɗaya ko kuma a sami ɗan banbanci ta dalilin yanayi ko zamani.


MAKKA:

A wunin  ranar Asabat 11/9/622 da tayi daidai da ran  29 ga Safar shekara ta 13 bayan Annabta shekara ta ɗaya na hijira, Mushirikan Makka da haɗin gwiwar Ibilis suka haɗu suka shirya tsaf domin kashe Annabin Musulunci Muhammad (S) da kuma musuluncin gaba ɗaya. Sai kuma a daren wunin  Asabat na  1/ 3/01H, watau shekara ta 13 bayan annabta. Wannan daren ya zama daren wunin Asabat 11/9/622M = 29/2/1H wannan haɗin gwiwa na Mushirikan Makka da Shaiɗan suka kaiwa Annabi Muhammad(S) hari, Asabat da dare da nufin kawo ƙarshen lamarinsa. Sai Allah cikin luɗufinsa ya tseratar dashi Annabi Muhammad(S) da sadaukarwar Imam Ali(A) da ya yarda ya bada rayuwarsa domin kariya ga shugabansa jagoransa Annabi Muhammad (S).


A wannan daran  ranar ɗaya ga Rabi'il Auwal Annabi Muhammad(S) ya bar gida zuwa kogon Hira da nufin yin Hijira zuwa Madina. Annabi Muhammad(S) ya kasance a cikin Kogon Hira na tsawon kusan wuni uku ko ince dare biyu da ɓangaren wuni, daren Asabat na 1/3/13B.A, da daren Lahadi 2/3/13 B.A, sai ɓangaern wunin Litinin da zai zo da daren 3/3/13B.A.  Aran Litinin Annabi Muhammad(S) suka kama hanyar babban Birnin Madina, shi da abokin tafiyarsa Makiyayi  masanin hanyar ratse mai suna Uraikiɗ bn Bakr addu'uliy


Daga nan kuma sai Annabi Muhammad(S) ya samu Nasara da samun kafa daular Musulunci na farko a wannan al'ummar a garin Madina. Kwanaki goma sha biyu(12) cif daga ranar Hijira. Nasara daga Allah tazo wa Annabi da Sahabbansa jarumai masu sadaukarwa, Aka yi fatahu Makkah watanni Tis'in da ɗaya (91) da yin hijira.


ZARIYA:

A binda ya mayar da wannan ranar ta hijira a Makka ta zama tayi kamanceceniya da al'amarin waƙi'ar Zariya a fahimta na shine kamar haka:


Kasantuwar kammala shirin Mahukuntan Nageriya yaran Uwar Shaiɗanu(Amerika) da gyauron Mushirikan Makka (Ali Sa'ud). Najeriya da haɗin bakinsu sun gama shirin su tsaf na himmar su akan kashe Saiyid Zakzaky a ran Juma'a 29/2/1437 da yayi daidai da ran 11/12/2015. A ranat Asabat 1/3/1437 da ya dace da Asabat 12/12/2015 wannan haɗin gwiwar na yaran Uwar shaiɗanu da gyauron mushirikan Makka suka kawo hari ga Saiyid Zakzaky a gidan sa dake Gyallesu a daren unin wannan tana ta Asabat, da nufin Kashe shi da kuma murƙushe kiran da yakeyi na neman tabbatuwar adalci a ƙasa ta Najeriya. Waƙi'ar ta ɗauki tsawon kusan wuni uku Asabat 1/3/1437, Lahadi 2/3/1437, Litinnin 3/3/1437 suka kama hanya da Saiyid Zakzaky zuwa babban birnin Najeriya.


Bayan da Saiyid Zakzaky ya shafe kusan tsawon wuni uku ko ince dare biyu da ɓangaren wunin Litinin a cikin gida ba tare da ya fito waje ba, kamar yanda ya kasance da Annabi Muhammad(S) a cikin Kogon Hira a lokacin yin Hijira. A wannan daren na Asabat na wunin 1/3/1437 Jaruman Sahabban Saiyid Zakzaky sun bayar da rayuwarsu sadaukarwa domin kariya ga rayuwar shugaba jagora, Kamar yanda Imam Ali(A) yayi a daren hijira


Watanni goma 12 da waƙi'ar ko ince da tafiya da Saiyid Zakzaky cif ba ragi ba ƙari, Saiyid Zakzaky ya samu nasara a Kotu akan mujiriman  mahukuntan ƙasarmu Najeriya a ranar Juma'a 3/3/1438 da ta dace da ranar Juma'a 2/12/2016.  A matakin " La yuhibbullahul jahara bissu'i illa man zulima " Ko yaushe ne ayar " Uzina lillazina yuƙatiluna bi annahum zulimu " zata fara aiki akanmu?  a garin Madinan Najeriya??? Wannan Allah ne masani.


A lokacin da Uraikiɗ bn Bakr addu'uliy yaji tsoron kar a gansu a kashe sai Annabi Muhammad (S) ya ce  masa: " Kar ka razana Allah yana tare damu " Haka shima Saiyid Zakzaky ya faɗa ga Husain da ya kira shi ta waya daga Iran, Saiyid Zakzkay yayi masa ishara da kar ya damu a inda yace: " .....ba abinda zan iya yi ga Allah kaɗai na dogara " Sanna kuma abin da yayi ta nuna ma ƴan'uwa da suke tare da shi kenan a lokacin. Kar ku damu Allah yana tare damu. Walla alla  kace ai shi Annabi ba a taɓa lafiyar jikinsa ba har aka zubar masa da jini. Tabbas haka ne amma biyoni muje filin Karbala acan ne zan baka amsa


KARBALA:

A gefe guda kuma waƙi'ar ta ran Asabat 12/12/2015 tayi kama da waƙi'ar Karbala na ran Asabat 10/10/680, ta fuskacin zubar da jini. An shahadantar da Imam Husain (A) da sahabbansa, amma sai Allah ya mayar dashi rayaiye a zukatan al'umma Musulmai da wasunsu daga wasu addinan. Sai ya zamana sakamakon zubar da jinin Imam Husain(A) sai cikakkiyar nasara mai ɗorewa ta samu ga wannan addinin nan musulunci.


Imam Husain(A) shine Galib akan Yazidu(L) amma nasarar Imam Husain(A) bazata samu ba har sai ta dalilin zubar jinin sa da kuma shahadantar dashi. Domin shahadar itace dalili na samun nasarar da ya samu.


Shi ma Saiyid Zakzaky shine Galib akan amma ta ina nasarar zata zo masa, wannan shine sanadin zubar jinin Saiyid Zakzaky da kuma raunata jikinsa. Wannan shine sanadin kammalar cikar nasarar shaharar lamarinsa da kuma tabbata. In ba mu manta ba ita waƙi'ar Zariya na 2015 tazo ne a lokacin Saiyid Zakzaky yana da shekara 64 da watanni 6. Mafi shaharar sunan Malam shine Zakzaky, Hisabin sunan Zakzaky shine 64 Sunan da ya samo asali daga sunan garin Zariya ( Zagzag) watau Zazzau. Hisabin sunan Zagzag da Malam ke Karɓa sunan sa da shi shine 2014, Ubangiji mafi iyawar masu lissafi sai ya sanya shekarar 2014 ta kasance shekarar farko na fara filfilawar sunan Zakaky a faɗin duniya daga shekarar zuwa yau. Sunan da yazama kusan ya shiga gidan kowa a faɗin wannan duniyar.


Kamar yanda kaifin Takobi ya sanya sanadin ɗaukakar sunan Imam Husain(A) da lamarin sa, da kuma wanzuwar addinin musulunci a faɗin duniya. Haka nan ma tsinin harsashin Bindiga ya zama sanadin ɗaukakar sunan Saiyid Zakzaky, kuma muke fatan hakan ya zama dalili na tabbatar adalcin addini a ɗaukacin wannan ƙasar tamu Najeriya.


Muna fatan wannan lamarin da su Saiyid Zakzaky suke ciki ya kasance mana shi ne hijirar da zasuyi wacce daga ita sai nasara na gaba ɗaya, Sllah ka tausaya mana. Kowannan sanadin shine zuwa na Musamman da Saiyid Zakzaky ya taɓa labarta mana da cewa: " Zamuyi wa Abuja zuwa na musamman "  Allah nr masani


Tabbas duk ranar 12 ga December na shekarar Miladiyya a kowace shekara zamu riƙa yin dafifi a dukkan biranen Nijeriya domin tuna wannan ta’adancin. Koda bayan ba ran  Genaral Buhari domin tuna masa mugun aikin sa tare da aika masa da kyautar addu'ar neman la'anar Allah zuwa gareshi da duk waɗanda suka taimaka masa, domin ninkuwar azabar Allah a garesu. kamar yanda a duk lokacin da muka la'anci Yazidu ɗan Mu'awiya Allah Ta'ala yana ƙara ninka masa azaba ne.


Muna fatan hakan ya zama sanadin la'antar Genaral Buhari har ƙarshen duniya. Kamar yanda hakan ya zama sanadin la'antar Yazidu har ƙarshen duniya.


Ya Allah ka gaggauta baiyanar  fitowa da tsayuwar lamarin Imam Mahdi (A) wanda da tsayuwarsa ne za a kawo ƙarshen zalunci da Azzalumai domin samuwar kammalalliyar Mulki na adalci a dukkan faɗin Duniya baki ɗaya. Da samar da wanzuwar la'antar Buhari da mataimakansa. Ya Allah ka kasance a tare da Ayatullahi Allama Saiyid Zakzaky (H) a duk in da yake ka bashi kariya ka makantar da tunani da idanuwan Azzaluman ƙasarmu akansa. Ya Allah ka gaggauta ɗaukar mana fansa albarkacin Imamul Asr (A). Ya Allah ka faranta mana rayukanmu da ganin ƙarshen maƙiyanmu. Ka tausaya ga wannan al’ummar, da ake zalunta ba dare ba rana.
.


04041440
12122018

12/12/2015

12/12/2015 BAKAR RANA GA MA'ABOTA TAUSAYI DA SANIN HAQQIN DAN ADAMTAKA!!!



Amincin Allah ya tabbata Ga Wanda yabi shiriya  da  goyon Bayan gaskiya da Adalci.

Ranar 12/12/2015 Ranace da tarihin Duniyar Mutane Bazai Manta da itaba ,Ranace data Kasance abar jimami da Zubar Hawaye Ga Ma'abota Neman Haqqi da son Gaskiya da Tabbatar Adalci, Rana Ce da ta Shahara da Ambato wajen Masana Haqqin Dan 'adamtaka ,Ranace Mai Cike da Ababen tausayi da tauye Haqqi ,Ranace da Rayukan Raunana  suka zama ababen Wulaqantawa  Ranace fa Jini  ya kwaranya A Magudanun Ruwa ,Ranace  da Yancin Dan' Adam Na rayuwa walwala da Haqqinsa Na  Mutumtaka Suka Saraya Daga Samuwa A Hannun Masu Mulkin kama karya Na Zalumci. a Nigeria Karkashin Mulkin Azzalumin Shugaba(General Buhari) Daya Sayar da Al'ummar Kasarsa Ga Bakin Haure  Masu Dagawa da tinkaho yan Mazhabar Shaidan (America, Israel da Saudi Arebia)Domin tabbatuwa akan Mulki  da Neman Duniya.

Shekara uku kenan cur da Kaddamar da Harin  ta'addancin Dabbobin Sojojin Nigeria akan Mutane  Raunana Maras Makami Na Harkar Musulumci a Nigeria da Jagoran ta Sayyed Zakzaky a Birnin Zaria Kaduna state, Harin  da yayi Sanadiyyar Kashe. Sama da Mutum 1000+ Almajiran Sayyed Zakzaky ciki har yayansa guda  Uku, tare da Rushe dukkan Wani Gini  ko Fili daya Zama Mallakin Hakar Musulumci kona  Jagoran ta, yayin Wannan Harin Gwamnatin Nigeria ta Rushe Babbar Cibiyar Harka  a Nigeria wajen bayar da ilimi da tarurrukan Addinin Musulumci wato (Hussainiyya Bakiyyatullah) Sun rushe Makabarta Inda Makwancin Shahidan Harkar Musulumci suke  ciki harda  tone kaburburan yayan jagoran Harkar Sayyed Zakzaky Wadanda Gwamnatin Ebele Jonathan ta kashe su yayin Muzaharar Nuna Goyon Baya  Ga Raunanan Al'ummar Palestine ta Duniya Wadda Aka Gabatar a Birnin Zaria A Shekarar 2014 .Gwamnatin Buhari ta rushe Gidan sheikh Zakzaky Da Makarantarsa wadda Qaton Library yake  ciki wadda Manyan Littafan Addinin Musulumci suke  ciki Wanda ya bada harda Littafin Allah Mai tsarki wato (Al Qur'an) Duk aka wulaqantasu yayin Wannan Hari da Gwamnatin Nigeria ta kaddamar Ga Harkar Musulumci

Gwamnatin Nigeria tayiwa Almajiran Sayyed Zakzaky Kabarin  bai daya (Massgrave) a garin Mando Kaduna state Inda sakataren Gwamnatin Kaduna ta Nasiru el Rufa'i ya bayyana cewa Sun Bizne Sama da Mutum 347 a Wannan ramin. 

Zalumcin Gwamnatin Buhari Bai tsaya nan ba Saidai suka  Qona Daruruwan Mutane da Wuta Ciki harda Yayar Sayyed Zakzaky Hajiya Fatima wadda suka Qonata da ranta a Gidan Sayyed Zakzaky da Ranta suka Banka Mata wuta Wanda Hakan yayi Sanadiyyar Shahadarta  ,

Sojojin Nigeria sun kama sama da Mutum 300+Almajiran Sayyed Zakzaky Amatsayin Fursunoni Wadanda suke  tsare dasu a gidajen yari Mabanbanta Na garin Kaduna Bisa Zalumci,

Jagoran Harkar Musulumci Sayyed Zakzaky ya samu Mummunan Harbin Bindiga a jikinsa shida Matarsa Malama Zeenat da Sojojin Nigeria sukayi Masu Wanda suke Cikin Mawuyacin Hali Na tsananin Rashin Lafiyar dake  damunsu tsawon Lokaci Batare da an kaisu Ga kwararren likita ba ana tsare dasu Bisa Zalumci a Hannun Hukumar jami'an tsaron  Farin kaya (DSS) Bisa Zalumci duk da cewa Babbar kotun tarayya dake  Abuja ta bayar da Umarnin sakin Sayyed da Mai dakinsa Malama Zeenat tun  ranar 2/12/2016 Kuma a Biyasu diyyar tsarewar Zalumci da akayi Masu  ta Naira Million Hamsin kuma a Gina Masu gida Inda suke so a duk Fadin arewacin Nigeria, Amma Har yanzu Gwamnatin Buhari tanayiwa Wannan doka da Umarnin kotun Karen tsaye da rashi  Mutumtawa  Wanda Har yanzu suna cigaba da tsare sheikh Zakzaky da Mai dakinsa Bisa Zalumci,

Bayan Win bin Umarnin kotu da Azzalumar Gwamnatin Buhari tayi  Na Sakin jagoran Harkar Musulumci Sayyed Zakzaky Sai Suka Shigar da Karar Sayyed Zakzaky da Matarsa da Wasu Almajiran Sa Gida Biyu Sheikh yaqub Yahaya katsina da Sheikh Dr.Sunusi Koki Kano) da Qirqirarrar Tuhumar Karya ta kisan  soja Daya  Cikin Dabbobin Sojojin Nigeria da Suka kaddamar kisan  kiyashi kan yan kasa  Raunana Na Harkar Musulumci a Nigeria Karkashin jagorancin  General Tukur Yusuf Burutai Bisa Umarnin Azzalumin Shugaban Nigeria General Buhari.

Wannan kadanne daga Zalumci Gwamnatin Buhari Ga Harkar Musulumci wadda Sheikh Zakzaky yakewa jagoranci a Wannan Bakar Rana ta 12/12/2015 Wanda Har yanzu ana cigaba dayinsa kan yan kasa  Almajiran Sayyed Zakzaky Kamar yanda y faru ranar 12/10/2018 a garin Abuja yayin da Mabiya Sayyed Zakzaky ke Gabatar da Ibadar Tattaki daga Masaka zuwa Abuja   Inda Dabbobin jami'an tsaron  Nigeria Suka kashe sama da Mutum 50+ tare da jikkata Fiye da Dari da kama sama da Mutum 400+ Bisa Zalumci.

Muna Allah wadai da wanna Nau'in Zalumci Na Azzalumar Gwamnatin Buhari.

Muna kira Ga Masana Haqqin Dan Adam da Hukomomi Na kasa  da kasa da Masu Son Gaskiya da Tabbatar Adalci Da Ma'abota Ruhin  tausayi dasu  Tilastawa Azzalumar Gwamnatin Buhari data bi  Umarnin kotu ta Saki Jagoran Harkar daga Tsare Zalumci shida duk Almajiran Sa a Fadin Nigeria

Bazamu yarda da duk Wani nuqu nuqu ba Na kashe Sayyed Zakzaky da Gwamnatin Buhari takeyi .

Rayukanmu fansane Ga rayuwar Sayyed Zakzaky. 

#FreeZakzaky


                

Tsokaci

Gwarazan Qarnin Nan sune, wadanda suka bayar/sadaukar da rayuwarsa, lokaci, jini da dukiya domin neman yardar Allah.
Kamar yadda Allah yake Fadi acikin Al-qur'ani Mai girma: 

Gabatarwa

GABATARWA:

Assalamu alaikum was rahmatullahi ta'ala wa barka tuhu. Muna qara godewa Allah subhanahu wa ta'ala a bisa ga dukkanin baiwa da ni'imomin da yayi mana. Tsira da aminci su tabbata ga Annabi Muhammad (s.a.w) da iyalan gidansa tsarkaka.