KAMAR MAKKAH KAMAR ZARIYA A RAN ƊAYA GA RABI'IL AUWAL 1437
Mahangar Shi'a ba tare da alfahari ba tana ƙunshe da nazarin da wata mahanga ba ta da shi, sannaj kuma ta keɓanta da al'amura da suke da dalili a hankalce saɓanin mafi yawan ra'ayoyin sauran mazhabobi da addinai.
YIWUWAR MAIMAICI:
Idan ma'aunin ilimi shi ne karɓar maimaici, to irin tashin Imam Mahdi (A) da tsayuwarsa don kafa daular adalci ta faru a lokuta masu yawa a zamanin farko kamar sauran sunnonin Allah. Don haka hukumarsa zata kasance wani ɓangare ne na sauran da suka gabata, tafarkin Imam Mahdi (A) da zuwan sa yayi kama da irin zuwan Annabi Musa (A), da Isa (A) da Muhammad (S)
Idan haka ne: Shin zai zama abin mamaki idan Allah ya kawo wani Musan wannan zamanin watau Imam Mahdi (A) da zai kawar da zaluncin da adalcinsa? da kuma taimaka masa da Harunansa zai yi, wato Annabi Isa (A), domin su kwance raunanan mutane daga ƙangin ɗaurin Fir'aunan zamani, su tseratar da su daga Dujal mai sihiri? Shin zai zama abin mamaki domin Allah ya sake tayar da wani mai tseratarwa ga ɗan Adam kamar yadda Muhammad Musɗafa (S) ya zo yana mai cewa: Kuce La'ilaha illallah!
( Shi'anci Da Duniyar Gobe. shafi na 106. littafin Dakta Ayat Kambari, Fassarar Dakta Hafiz Muhammad Sa'id Kano)
In mukayi la'akari da abin da ya gabata daga littafin Shi'anci da Duniyar gobe, na yiwuwar samun maimaicin lamura a rayuwar ɗan adam, za muga cewa a wannan yankin na ƙasar tamu an taɓa samun wani Mujaddidi da ya sabunta lamarin addini a wannan nahiyar aka wanzu a cikin adalcin mahalicci. Haƙiƙa ba abin mamaki bane sake ganin wani da zai maimaita wancan yanayin na Shehu Usman ɗan Fodiye da ya gabata sama da shekatu 200.
Maganar Sayyid Zakzaky, in muka lura , domin bayan ya fara kira akan kalmar Tauhidi, (Babu hukuma sai ta Allah) wannan ya karɓu har tafiyar ta koma Jafariyanci to ya ci gaba da kira ne akan tabbatar da adalci, da rushe zalunci ga kowane ɗan Adam ba lallai Musulmi ba. Wanda shi ya janyo a yanzu haka cikin tafiyar ta haɗa da Shi'a da Sunna, da ma wasu addinin Kitistanci harma da waɗanda suke musanta samuwar Allah daga masu ƙyamar zalunci sunantarr da harkar da Saiyid Zakzaky ke jagoranta a Nijeriya. Don gwagwarmayar kuɓutar da al'umma daga zaluncin da suke ciki. Wanda wannan shine farko tushen da Imamul-Hujjah (A) zai yi yaƙi a kai, na kawar da azzalumai da zalunci da tallafawa waɗanda ake zalunta na duniya baki ɗaya daga kowane tafarki. Shi yasa ma hadisai suka tabbatar har da Kiristoci a mataimakansa da masu bautar rana, don haka ne a na kusa da shi Imam Mahdi (A) Masihu Isa ɗan Maryam(A) ne ga kuma Khidir (A).
Haƙiƙa tarihi yakan maimaita kansa ta fuskoki da daman gaske. Domin ita wannan rayuwar takan jujjuya ne a tsakain mutane. Watau akan samu maimaicin yanayin rayuwa a tsakanin wata al'ummar da wata data biyo bayanta a wani zamanin ko ƙarni a wani lokaci ta wasu fuskokin walau iri ɗaya ko kuma a sami ɗan banbanci ta dalilin yanayi ko zamani.
MAKKA:
A wunin ranar Asabat 11/9/622 da tayi daidai da ran 29 ga Safar shekara ta 13 bayan Annabta shekara ta ɗaya na hijira, Mushirikan Makka da haɗin gwiwar Ibilis suka haɗu suka shirya tsaf domin kashe Annabin Musulunci Muhammad (S) da kuma musuluncin gaba ɗaya. Sai kuma a daren wunin Asabat na 1/ 3/01H, watau shekara ta 13 bayan annabta. Wannan daren ya zama daren wunin Asabat 11/9/622M = 29/2/1H wannan haɗin gwiwa na Mushirikan Makka da Shaiɗan suka kaiwa Annabi Muhammad(S) hari, Asabat da dare da nufin kawo ƙarshen lamarinsa. Sai Allah cikin luɗufinsa ya tseratar dashi Annabi Muhammad(S) da sadaukarwar Imam Ali(A) da ya yarda ya bada rayuwarsa domin kariya ga shugabansa jagoransa Annabi Muhammad (S).
A wannan daran ranar ɗaya ga Rabi'il Auwal Annabi Muhammad(S) ya bar gida zuwa kogon Hira da nufin yin Hijira zuwa Madina. Annabi Muhammad(S) ya kasance a cikin Kogon Hira na tsawon kusan wuni uku ko ince dare biyu da ɓangaren wuni, daren Asabat na 1/3/13B.A, da daren Lahadi 2/3/13 B.A, sai ɓangaern wunin Litinin da zai zo da daren 3/3/13B.A. Aran Litinin Annabi Muhammad(S) suka kama hanyar babban Birnin Madina, shi da abokin tafiyarsa Makiyayi masanin hanyar ratse mai suna Uraikiɗ bn Bakr addu'uliy
Daga nan kuma sai Annabi Muhammad(S) ya samu Nasara da samun kafa daular Musulunci na farko a wannan al'ummar a garin Madina. Kwanaki goma sha biyu(12) cif daga ranar Hijira. Nasara daga Allah tazo wa Annabi da Sahabbansa jarumai masu sadaukarwa, Aka yi fatahu Makkah watanni Tis'in da ɗaya (91) da yin hijira.
ZARIYA:
A binda ya mayar da wannan ranar ta hijira a Makka ta zama tayi kamanceceniya da al'amarin waƙi'ar Zariya a fahimta na shine kamar haka:
Kasantuwar kammala shirin Mahukuntan Nageriya yaran Uwar Shaiɗanu(Amerika) da gyauron Mushirikan Makka (Ali Sa'ud). Najeriya da haɗin bakinsu sun gama shirin su tsaf na himmar su akan kashe Saiyid Zakzaky a ran Juma'a 29/2/1437 da yayi daidai da ran 11/12/2015. A ranat Asabat 1/3/1437 da ya dace da Asabat 12/12/2015 wannan haɗin gwiwar na yaran Uwar shaiɗanu da gyauron mushirikan Makka suka kawo hari ga Saiyid Zakzaky a gidan sa dake Gyallesu a daren unin wannan tana ta Asabat, da nufin Kashe shi da kuma murƙushe kiran da yakeyi na neman tabbatuwar adalci a ƙasa ta Najeriya. Waƙi'ar ta ɗauki tsawon kusan wuni uku Asabat 1/3/1437, Lahadi 2/3/1437, Litinnin 3/3/1437 suka kama hanya da Saiyid Zakzaky zuwa babban birnin Najeriya.
Bayan da Saiyid Zakzaky ya shafe kusan tsawon wuni uku ko ince dare biyu da ɓangaren wunin Litinin a cikin gida ba tare da ya fito waje ba, kamar yanda ya kasance da Annabi Muhammad(S) a cikin Kogon Hira a lokacin yin Hijira. A wannan daren na Asabat na wunin 1/3/1437 Jaruman Sahabban Saiyid Zakzaky sun bayar da rayuwarsu sadaukarwa domin kariya ga rayuwar shugaba jagora, Kamar yanda Imam Ali(A) yayi a daren hijira
Watanni goma 12 da waƙi'ar ko ince da tafiya da Saiyid Zakzaky cif ba ragi ba ƙari, Saiyid Zakzaky ya samu nasara a Kotu akan mujiriman mahukuntan ƙasarmu Najeriya a ranar Juma'a 3/3/1438 da ta dace da ranar Juma'a 2/12/2016. A matakin " La yuhibbullahul jahara bissu'i illa man zulima " Ko yaushe ne ayar " Uzina lillazina yuƙatiluna bi annahum zulimu " zata fara aiki akanmu? a garin Madinan Najeriya??? Wannan Allah ne masani.
A lokacin da Uraikiɗ bn Bakr addu'uliy yaji tsoron kar a gansu a kashe sai Annabi Muhammad (S) ya ce masa: " Kar ka razana Allah yana tare damu " Haka shima Saiyid Zakzaky ya faɗa ga Husain da ya kira shi ta waya daga Iran, Saiyid Zakzkay yayi masa ishara da kar ya damu a inda yace: " .....ba abinda zan iya yi ga Allah kaɗai na dogara " Sanna kuma abin da yayi ta nuna ma ƴan'uwa da suke tare da shi kenan a lokacin. Kar ku damu Allah yana tare damu. Walla alla kace ai shi Annabi ba a taɓa lafiyar jikinsa ba har aka zubar masa da jini. Tabbas haka ne amma biyoni muje filin Karbala acan ne zan baka amsa
KARBALA:
A gefe guda kuma waƙi'ar ta ran Asabat 12/12/2015 tayi kama da waƙi'ar Karbala na ran Asabat 10/10/680, ta fuskacin zubar da jini. An shahadantar da Imam Husain (A) da sahabbansa, amma sai Allah ya mayar dashi rayaiye a zukatan al'umma Musulmai da wasunsu daga wasu addinan. Sai ya zamana sakamakon zubar da jinin Imam Husain(A) sai cikakkiyar nasara mai ɗorewa ta samu ga wannan addinin nan musulunci.
Imam Husain(A) shine Galib akan Yazidu(L) amma nasarar Imam Husain(A) bazata samu ba har sai ta dalilin zubar jinin sa da kuma shahadantar dashi. Domin shahadar itace dalili na samun nasarar da ya samu.
Shi ma Saiyid Zakzaky shine Galib akan amma ta ina nasarar zata zo masa, wannan shine sanadin zubar jinin Saiyid Zakzaky da kuma raunata jikinsa. Wannan shine sanadin kammalar cikar nasarar shaharar lamarinsa da kuma tabbata. In ba mu manta ba ita waƙi'ar Zariya na 2015 tazo ne a lokacin Saiyid Zakzaky yana da shekara 64 da watanni 6. Mafi shaharar sunan Malam shine Zakzaky, Hisabin sunan Zakzaky shine 64 Sunan da ya samo asali daga sunan garin Zariya ( Zagzag) watau Zazzau. Hisabin sunan Zagzag da Malam ke Karɓa sunan sa da shi shine 2014, Ubangiji mafi iyawar masu lissafi sai ya sanya shekarar 2014 ta kasance shekarar farko na fara filfilawar sunan Zakaky a faɗin duniya daga shekarar zuwa yau. Sunan da yazama kusan ya shiga gidan kowa a faɗin wannan duniyar.
Kamar yanda kaifin Takobi ya sanya sanadin ɗaukakar sunan Imam Husain(A) da lamarin sa, da kuma wanzuwar addinin musulunci a faɗin duniya. Haka nan ma tsinin harsashin Bindiga ya zama sanadin ɗaukakar sunan Saiyid Zakzaky, kuma muke fatan hakan ya zama dalili na tabbatar adalcin addini a ɗaukacin wannan ƙasar tamu Najeriya.
Muna fatan wannan lamarin da su Saiyid Zakzaky suke ciki ya kasance mana shi ne hijirar da zasuyi wacce daga ita sai nasara na gaba ɗaya, Sllah ka tausaya mana. Kowannan sanadin shine zuwa na Musamman da Saiyid Zakzaky ya taɓa labarta mana da cewa: " Zamuyi wa Abuja zuwa na musamman " Allah nr masani
Tabbas duk ranar 12 ga December na shekarar Miladiyya a kowace shekara zamu riƙa yin dafifi a dukkan biranen Nijeriya domin tuna wannan ta’adancin. Koda bayan ba ran Genaral Buhari domin tuna masa mugun aikin sa tare da aika masa da kyautar addu'ar neman la'anar Allah zuwa gareshi da duk waɗanda suka taimaka masa, domin ninkuwar azabar Allah a garesu. kamar yanda a duk lokacin da muka la'anci Yazidu ɗan Mu'awiya Allah Ta'ala yana ƙara ninka masa azaba ne.
Muna fatan hakan ya zama sanadin la'antar Genaral Buhari har ƙarshen duniya. Kamar yanda hakan ya zama sanadin la'antar Yazidu har ƙarshen duniya.
Ya Allah ka gaggauta baiyanar fitowa da tsayuwar lamarin Imam Mahdi (A) wanda da tsayuwarsa ne za a kawo ƙarshen zalunci da Azzalumai domin samuwar kammalalliyar Mulki na adalci a dukkan faɗin Duniya baki ɗaya. Da samar da wanzuwar la'antar Buhari da mataimakansa. Ya Allah ka kasance a tare da Ayatullahi Allama Saiyid Zakzaky (H) a duk in da yake ka bashi kariya ka makantar da tunani da idanuwan Azzaluman ƙasarmu akansa. Ya Allah ka gaggauta ɗaukar mana fansa albarkacin Imamul Asr (A). Ya Allah ka faranta mana rayukanmu da ganin ƙarshen maƙiyanmu. Ka tausaya ga wannan al’ummar, da ake zalunta ba dare ba rana.
.
04041440
12122018

No comments:
Post a Comment