Followers

Tuesday, March 5, 2019

12/12/2015

12/12/2015 BAKAR RANA GA MA'ABOTA TAUSAYI DA SANIN HAQQIN DAN ADAMTAKA!!!



Amincin Allah ya tabbata Ga Wanda yabi shiriya  da  goyon Bayan gaskiya da Adalci.

Ranar 12/12/2015 Ranace da tarihin Duniyar Mutane Bazai Manta da itaba ,Ranace data Kasance abar jimami da Zubar Hawaye Ga Ma'abota Neman Haqqi da son Gaskiya da Tabbatar Adalci, Rana Ce da ta Shahara da Ambato wajen Masana Haqqin Dan 'adamtaka ,Ranace Mai Cike da Ababen tausayi da tauye Haqqi ,Ranace da Rayukan Raunana  suka zama ababen Wulaqantawa  Ranace fa Jini  ya kwaranya A Magudanun Ruwa ,Ranace  da Yancin Dan' Adam Na rayuwa walwala da Haqqinsa Na  Mutumtaka Suka Saraya Daga Samuwa A Hannun Masu Mulkin kama karya Na Zalumci. a Nigeria Karkashin Mulkin Azzalumin Shugaba(General Buhari) Daya Sayar da Al'ummar Kasarsa Ga Bakin Haure  Masu Dagawa da tinkaho yan Mazhabar Shaidan (America, Israel da Saudi Arebia)Domin tabbatuwa akan Mulki  da Neman Duniya.

Shekara uku kenan cur da Kaddamar da Harin  ta'addancin Dabbobin Sojojin Nigeria akan Mutane  Raunana Maras Makami Na Harkar Musulumci a Nigeria da Jagoran ta Sayyed Zakzaky a Birnin Zaria Kaduna state, Harin  da yayi Sanadiyyar Kashe. Sama da Mutum 1000+ Almajiran Sayyed Zakzaky ciki har yayansa guda  Uku, tare da Rushe dukkan Wani Gini  ko Fili daya Zama Mallakin Hakar Musulumci kona  Jagoran ta, yayin Wannan Harin Gwamnatin Nigeria ta Rushe Babbar Cibiyar Harka  a Nigeria wajen bayar da ilimi da tarurrukan Addinin Musulumci wato (Hussainiyya Bakiyyatullah) Sun rushe Makabarta Inda Makwancin Shahidan Harkar Musulumci suke  ciki harda  tone kaburburan yayan jagoran Harkar Sayyed Zakzaky Wadanda Gwamnatin Ebele Jonathan ta kashe su yayin Muzaharar Nuna Goyon Baya  Ga Raunanan Al'ummar Palestine ta Duniya Wadda Aka Gabatar a Birnin Zaria A Shekarar 2014 .Gwamnatin Buhari ta rushe Gidan sheikh Zakzaky Da Makarantarsa wadda Qaton Library yake  ciki wadda Manyan Littafan Addinin Musulumci suke  ciki Wanda ya bada harda Littafin Allah Mai tsarki wato (Al Qur'an) Duk aka wulaqantasu yayin Wannan Hari da Gwamnatin Nigeria ta kaddamar Ga Harkar Musulumci

Gwamnatin Nigeria tayiwa Almajiran Sayyed Zakzaky Kabarin  bai daya (Massgrave) a garin Mando Kaduna state Inda sakataren Gwamnatin Kaduna ta Nasiru el Rufa'i ya bayyana cewa Sun Bizne Sama da Mutum 347 a Wannan ramin. 

Zalumcin Gwamnatin Buhari Bai tsaya nan ba Saidai suka  Qona Daruruwan Mutane da Wuta Ciki harda Yayar Sayyed Zakzaky Hajiya Fatima wadda suka Qonata da ranta a Gidan Sayyed Zakzaky da Ranta suka Banka Mata wuta Wanda Hakan yayi Sanadiyyar Shahadarta  ,

Sojojin Nigeria sun kama sama da Mutum 300+Almajiran Sayyed Zakzaky Amatsayin Fursunoni Wadanda suke  tsare dasu a gidajen yari Mabanbanta Na garin Kaduna Bisa Zalumci,

Jagoran Harkar Musulumci Sayyed Zakzaky ya samu Mummunan Harbin Bindiga a jikinsa shida Matarsa Malama Zeenat da Sojojin Nigeria sukayi Masu Wanda suke Cikin Mawuyacin Hali Na tsananin Rashin Lafiyar dake  damunsu tsawon Lokaci Batare da an kaisu Ga kwararren likita ba ana tsare dasu Bisa Zalumci a Hannun Hukumar jami'an tsaron  Farin kaya (DSS) Bisa Zalumci duk da cewa Babbar kotun tarayya dake  Abuja ta bayar da Umarnin sakin Sayyed da Mai dakinsa Malama Zeenat tun  ranar 2/12/2016 Kuma a Biyasu diyyar tsarewar Zalumci da akayi Masu  ta Naira Million Hamsin kuma a Gina Masu gida Inda suke so a duk Fadin arewacin Nigeria, Amma Har yanzu Gwamnatin Buhari tanayiwa Wannan doka da Umarnin kotun Karen tsaye da rashi  Mutumtawa  Wanda Har yanzu suna cigaba da tsare sheikh Zakzaky da Mai dakinsa Bisa Zalumci,

Bayan Win bin Umarnin kotu da Azzalumar Gwamnatin Buhari tayi  Na Sakin jagoran Harkar Musulumci Sayyed Zakzaky Sai Suka Shigar da Karar Sayyed Zakzaky da Matarsa da Wasu Almajiran Sa Gida Biyu Sheikh yaqub Yahaya katsina da Sheikh Dr.Sunusi Koki Kano) da Qirqirarrar Tuhumar Karya ta kisan  soja Daya  Cikin Dabbobin Sojojin Nigeria da Suka kaddamar kisan  kiyashi kan yan kasa  Raunana Na Harkar Musulumci a Nigeria Karkashin jagorancin  General Tukur Yusuf Burutai Bisa Umarnin Azzalumin Shugaban Nigeria General Buhari.

Wannan kadanne daga Zalumci Gwamnatin Buhari Ga Harkar Musulumci wadda Sheikh Zakzaky yakewa jagoranci a Wannan Bakar Rana ta 12/12/2015 Wanda Har yanzu ana cigaba dayinsa kan yan kasa  Almajiran Sayyed Zakzaky Kamar yanda y faru ranar 12/10/2018 a garin Abuja yayin da Mabiya Sayyed Zakzaky ke Gabatar da Ibadar Tattaki daga Masaka zuwa Abuja   Inda Dabbobin jami'an tsaron  Nigeria Suka kashe sama da Mutum 50+ tare da jikkata Fiye da Dari da kama sama da Mutum 400+ Bisa Zalumci.

Muna Allah wadai da wanna Nau'in Zalumci Na Azzalumar Gwamnatin Buhari.

Muna kira Ga Masana Haqqin Dan Adam da Hukomomi Na kasa  da kasa da Masu Son Gaskiya da Tabbatar Adalci Da Ma'abota Ruhin  tausayi dasu  Tilastawa Azzalumar Gwamnatin Buhari data bi  Umarnin kotu ta Saki Jagoran Harkar daga Tsare Zalumci shida duk Almajiran Sa a Fadin Nigeria

Bazamu yarda da duk Wani nuqu nuqu ba Na kashe Sayyed Zakzaky da Gwamnatin Buhari takeyi .

Rayukanmu fansane Ga rayuwar Sayyed Zakzaky. 

#FreeZakzaky


                

No comments:

Post a Comment